✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama shi kan azabtar da ’yar aiki da wuta kan keken ’ya’yansa

Mutumin ya sa karfe a wuta ya rika yi wa yarinya mai shekara 12 lalas da shi saboda zargin ta hau keken ’ya’yansa.

Wani magidanci ya shiga hannu kan yi wa ’yar aikinsa azaba da karfen da aka sanya a wuta bisa zargin hawa keken ’ya’yansa.

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Imo ta cafke magidancin ne bayan ya sanya karfe a wuta, ya rika yi wa yarinyar mai shekara 12 lalas da shi a mazaunanta.

An tsare mutumin ne da taimakon wani mai rajin kare hakkin dan Adam, Darlington Chidera Ibekwe, bayan bidiyon aika-aikan da mutumin ya aikata ya karade kafofin sada zumunta na zamani.

Kakakin ’yan sandan jihar, Mike Abattam, ya shaida wa wakilinmu cewa magidancin na tsare a Ofishin ’Yan Sanda na New Owerri, muka za a mika shi domin amsa tambayoyi a Sashen Binciken Manyan Laifuka na rundunar.

Jami’in ya ce an kai karamar yarinyar asibiti domin ba ta kulawa.