An kama shi ya yi wa yara ’yan uwan juna fyade | Aminiya

An kama shi ya yi wa yara ’yan uwan juna fyade

Fyade
Fyade
    Eugene Agha, Legas da Sagir Kano Saleh

Wani mai shekara 35 ya shiga hannun ’yan sanda bayan ya yi wa wasu yara ’yan uwan juna fyade.

A sakamakon fyaden da ya yi wa yaran masu shekara 13 da 16 ne babbar cikinsu ta dauki juna biyu.

“Mahaifiyar yaran ce ta kawo korafi cewa ya yi wa ’yarta mai shekara 16, kanwarta mai sheka 13 kuma ya yi mata fyade,” inji ’yan sanda a Jihar Detla, inda abin ya faru.

Kakakin Rundunar Delta, Edafe Brighti, ya ce mutumin ya yaudari yaran ne a lokuta daban-daban ya sadu da su.

Ya ce, lamarin ay faru ne a yakin tiktin Okpanam, da ke jihar, kuma wanda ake zargin ya amsa laifinsa.

“A wurin bincike ya masa laifin da ake zargin ya aikata. An yi wa yaran gwaji a asibiti, shi kuma yana tsare ana ci gaba da bincike, da zarar an kammala za a gurfanar da shi a gaban kuliya,” inji Edafe.

Ya ce a sakamkon korafin ne Kwamishin ’Yan Sandan Jihar, Ali Mohammed Ari, ya sa kamo wanda ake zargin.