✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama soja yana fashi da makami a Yobe

Shi da abokansa sun yi wa wata mata fashin kudi da mota a garin Damaturu

Dubun wani soja ta da ke aikata fashi da makami ta cika inda aka kama shi tare da wasu mutum biyu bayan sun yi fashi a garin Damaturu, Jihar Yobe.

’Yan Sanda sun cafke sojan da abokan fashin nasa ne bayan sun kutsa gida wata mata a unguwar Sabon Pegi da tsakar dare dauke da bindiga kirar AK 47 da sauran muggan makamai suka yi mata fashi.

An kama sojan da abokan fashinsa ne bayan sun yi wa matar awon gaba da mota kirar Peugeot 307 da tsabar kudi N250,000 da kuma wayar hannu kirar Nokia.

“Bayan an kama su, sun shaida wa ’yan sanda masu bincike cewa suna so ne su sayar da motar su raban kudin; Za a gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala bincike,” inji Kakakin ’Yan Sandan Jihar Yobe, ASP Dungus Abdulkarim.

Ya kara da cewa ’yan fashin sun yi wa matar da danta mai shekara 17 rauni bayan sun daure su da wata waya a jikin turken faifen dauraron dan Adam.

ASP Dungus ya bayyana cewa an kama biyu daga cikin ’yan fashin ne a garin Damaturu, na ukunsu kuma wanda motar take hannunsa an kama shi ne a garin Darazo na Jihar Bauchi.

Ya ce ’yan sanda sun yi nasarar kwace makaman ’yan fashin da kuma duk kayan da suka yi fashi a gidan da suka shiga.

Ya bayyana cewa sojan da aka maka yana aiki ne da Runduna ta 2 karkashin Rundunar Operation Hadin Kai da ke aiki a Damaturu, sauran kuma matasa ne da ke zaune a garin.

Yanzu haka sojan da abokan fashin nasa suna fuskantar zargin shiga gida ba da izini ba, aikata fashi da makami da sauran laifuka.

A cewarsa, Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Yobe, Haruna Garba, ya shawarci mazauna jihar da su kasance masu lura a abin da faruwa a zagaye da su, tare da taimaka wa jami’an tsaro da muhimman bayanai domin magance miyagun laifuka.