✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama uwa da ‘ya’yanta a kan fashi da makami a Kano

An kwace bindigogi da kakin sojoji a hannun 'yan fashin a jihar Kano.

Wata tsohuwa mai shekaru 60 ta shiga hannu tare da ‘ya’yanta guda biyu bisa zargin fashi da makami a Jihar Kano.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, CP Habu Sani ya ce samamen ‘yan sanda a gidan mutanen ya gano bindigogi uku da kakin sojoji.

“Bayan bincike, mun gano bindigogi kirar AK-47 guda biyu da albarusai 41 da wata bindiga kuma dauke da albarusai hudu da kuma jakin sojoji”, inji shi.

Ya ce an kama ‘yan fashin ne bayan sun kai hari a gidan wani mutum wanda suka yi wa awon gaba da Naira dubu dari hudu a kauyen Rantan da ke Karamar Hukumar Bebeji.

Ya ce karin bincike ya kai ga tsare mahaifiyar matasan ‘yar shekara 60, wadda take ta kokarin kawar da shaidar da ke nuna cewa ‘ya’yan nata sun yi laifin.

Rundunar ta kuma tsare kanin mutumin da aka yi wa fashin bisa zargin hannunsa a ciki.

Tsohuwar da ‘ya’yan nata na daga cikin masu laifi 392 da rundunar ta gabatar wa ‘yan jarida a ranar Alhamis.

Habu Sani ya ce mutanen da ake wa zargin fashin sun amsa laifin da ake tuhumar su da aikatawa.