An kama wanda ya yi wa yarinya fyade har ta mutu | Aminiya

An kama wanda ya yi wa yarinya fyade har ta mutu

    Ishaq Isma'il da Eugene Agha Lagos

An kama wani matashi mai shekara 24 bisa zargin sace wata budurwa ’yar shekara 13, da kuma yayi mata fyade har ta mutu a yankin Ejigbo na Jihar Legas.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas, Muyiwa Adejobi a cikin wata sanarwa ya ce abokanan matashin biyu da suka aikata ta’asar tare tuni sun cika bujensu da iska.

Sanarwar ta ce matasan uku sun yi wa budurwar jina-jina a fyaden da suka yi mata a wani daki, suka kama tafi suka kyale ta har ta mutu.

Rundunar ta ce a yayin da saurayin ke tsare a sashen binciken miyagun laifuka a reshenta da ke kan titin Panti, Yaba, an baza jami’ai domin taso keyar sauran masu ta’adar barnar.

Mista Adejobi ya ce matasan sun aikata mummunar ta’adar ne a ranar 30 ga watan Satumba, bayan mahifiyar yarinyar ta aike ta da misalin karfe 10.30 na dare.