✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wani mutum ya yi yarinya fyade a coci

Ya amsa cewa  ya yi wa budurwar mai shekara 18 fyade a harabar coci

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ogun ta kama wani mutum bisa zargin shi da yi wa wata budurwa fyade a harabar coci.

Dubunsa ta cika ne bayan mika rahoton da mahaifiyar wadda abin ya faru a kanta ta yi ga ofishin ’yan sandan da ke yankin Lafenwa a Abeokuta.

Nan take DPO ya baza komar jami’an bincike domin kamo wanda ake zargin, wanda aka yi ram da shi ranar Alhamis, 21 ga Afrilu, 2022.

Da aka tsiye shi a wurin bincike, ya amsa laifinsa, cewa  ya yi wa budurwar mai shekara 18 fyade a harabar coci.

Kakakin ’yan sandan Jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Lanre Bankole ya bada umarni a mika wanda ake zargin ga Sashen Binciken Manyan Laifuka na rundunar ta gudanar da cikakken bincike sannan a gurfanar da shi a gaban kotu.