✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama ’yan kasar waje masu safarar A Kurkura

NDLEA a kama nakasasshe da curin tabar wiwi mai nauin kilgoram 104

Wasu ’yan kasar Mali guda biyu sun shiga hannu a yayin da suke kokarin fasakwaurin maganin na mai galabaia mutane da ake kira A Kurkura zuwa daga Najeria.

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoiy ta Kasa (NDLEA) a kuma kama wani nakasasshe da ke dillancin miyagun kwayoyi, inda ta kwace curin tabar wiwi mai nauin kilgoram 104 a hannunsa a Jihar Ogun.

Kakakin NDLEA, Femi Babafemi, ya ce, jami’an hukumar sun kama ’yan kasar Malin ne da Kilogram  34.2 na kwalaben A Kurkura suna kokarin kaiwa kasarsu a Kwatano, Jamhuriar Benin.

Jami’an NDLEA sun kuma kama wani wata ’yar kasuwa mai shekara 32 a filin jirgin sama na Abuja ana kokarin safarar miyagun kwayoyin Rahynol  zuwa birnin Santanbul na kasa Turkiyyya, inda ake da gidan abinci.

A ranar Alhamis kuma hukumar ta kwace curi 100 na tabar wiwi mai nauyin kilogram 73.5, da aka boye cikin abincin dabbobi a Jihar Taraba.

Babafemi ya ce sun kuma kama waa mata da kilogram 27 na miyagun kwaoyi.

Shugaban Hukumar NDLEA, Mohamed Buba Marwa ya yaba wa jami’an bisa kamun da suka yi, ya mai kiran su da su kara jajircewa wajen dakile ayyukan masu fataucin miyagun kwayoyi da dangoginsu a Najeriya.