✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kammala daukar shirin Labarina zango na uku

Ana jiran ranar da za a fara haskawa da kuma inda da za a haska

An kammala daukar fitaccen shirin nan mai dogon zango, Labarina, zango na uku.

Daraktan shirin, Aminu Saira ne ya bayyana hakan a shafinsa na Instagram.

A shafin nasa, Aminu Saira ya wallafa cewa, “Alhamdulillah. Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Cikin yardar Ubangiji mun kammala daukar shirin Labarina zango na uku.

“Muna godiya ga duk wadanda suka bayar da gudunmawa wajen kammaluwar aikin.

“Yanzu abin da ya rage shi ne ranar da za a fara haskawa da kuma inda da za a haska shi.

“Cikin kwanaki kadan za mu sanar in sha’a Allah. Allah Ka sa mu fita kunyar masu kallo,” a cewar sakon

Shirin Labarina dai ya dauki hankalin mutane matuka, inda hatta manyan ma’aikatan gwamnati da ’yan siyasa ba a bar su a baya ba, yayin da maganar shirin ta rika gudana a kan harsunansu.

An je hutu ne bayan an kammala haska zango na biyu shirin, inda lokacin masu kallo suke ta dakon ranar da za a dawo.

 

View this post on Instagram

 

A post shared by Aminu Saira (@aminusaira)