✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kammala gasar cin kofin Ciyaman din Kaduna ta Arewa

Kungiyar Goldeen Bees FC ta Unguwar Liman

A ranar Lahadi ce aka buga wasan karshe na Gasar Cin Kofin Shugaban Kaduna ta Arewa, Mukhtar Baloni, ta bana.

Kungiyar Goldeen Bees FC ta Unguwar Liman ce ta lashe kofin, bayan ta doke kungiyar Emirates FC ta Unguwar Rimi a wasan karshe.

Haka kuma kungiyar Dosa Dynamite FC ta Unguwar Dosa ce ta zo ta uku.

Da yake jawabi wajen wasan na karshe, Aminiya ta ruwaito Shugaban Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa, Mukhtar Baloni shirya gasar, wadda ya ce karon farko da aka shirya gasar da aka shirya domin samun hadin kan matasa tare da taimakonsu wajen kai wa ga bantensu a harkar ta kwallo.

Alhaji Mukhtar Baloni ya ce za su cigaba da shirya irin wannan gasar da wasu hanyoyin tallafawa matasa da mata da sauran mutane.