✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kammala jefe kuri’ar zaben fid-da gwanin APC

Daliget 2,340 daga jihohi 36 da kuma Abuja sun shafe kusan awa biyar suna jefa kuri'a

Daliget sun kammala jefa kuri’a a zaben fid-da dan takarar shugaban kasa da jam’iyyar APC ke gudanarwa a Abuja.

An kammala zaben ne bayan daliget 2,340 daga Abuja da jihohi 36 na Najeriya sun shafe kusan awa biyar suna jefa kuri’a tun daga misalin karfe 2 na dare.

Yanzu bayan kammala jefa kuri’ar, kwamitin zaben zai tantance su sannan a kirga, a kuma sanar da yawan kuri’un da kowane dan takara ya samu, da kuma wanda ya zama gwani.

Tun da farko dai zaben ya dan samu tsaiko na kusan minti 30 saboda batun daliget, inda aka ga tsohon Ministan Sufuri kuma dan takara, Rotimi Amaechi suna cacar baki da wakilan ’yan takara.

Kafin barin zauren taron da misalin karfe 1.20, wato kafin fara zaben, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bukaci mambobin APC da su hada kai su zabo dan takara mai farin jini da kishin kasa kuma haziki wanda zai kai jam’iyyarsu ga nasara a babban zaben 2023.

Jerin mutum 14 ne dai sauka fafata a zaben neman tikitin takarar kujera mafi girma a Najeriya:

  1. Tsohon Gwamnan Jihar Legas,  Bola Ahmed Tinubu
  2. Mataimakin shugaban Kasa Yemi Osinbajo
  3. Shugaban Majalisar Dattawa, Santa Ahmad Lawan
  4. Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi
  5. Tsohon Ministan Kimiyya da Fasa, Ogbonnaya Onu
  6. Tsohon Gwamnan Jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha
  7. Gwamnan Jihar Ebonyi, Dave Umahi
  8. Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello
  9. Hamshakin attajiri, Tein Jack-Rich
  10. Tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa, Fasto Tunde Bakare
  11. Tsohon Minista a Ma’aikatar Ilimi, Emeka Nwajiuba
  12. Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Ahmed Sani Yarima
  13. Gwamnan Jihar Kuros Riba, Farfesa Ben Ayade da kuma
  14. Ikeobasi Mokhelu.

Mutum 14 sun fatata ne bayan bakwai daga cikin ’yan takara 23 sun janye wa Tinubu sa’o’i kadan kafin zaben, a yayin da mutum daya ya jaye wa Osinbajo.