✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kara farashin wutar lantarki a Najeriya

Duk da matsin tattalin arziki da ake fama da shi sakamakon cutar COVID-19, kamfanonin rarraba hasken wutar lantarki sun kara kudin wutar a Najeriya. Hakan…

Duk da matsin tattalin arziki da ake fama da shi sakamakon cutar COVID-19, kamfanonin rarraba hasken wutar lantarki sun kara kudin wutar a Najeriya.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da wa’adin da aka diba na jinkirta yin karin yake cika ranar Talata.

Tuni dai rahotanni suka tabbatar da cewa akalla kamfanoni uku sun kara farashin kamar yadda Hukumar Kula da Hasken Lantarki ta Kasa (NERC) ta amince.

A baya dai NERC ta ce dole kamfanonin su nemi amincewar abokan huldarsu kafin yin karin tare kuma da cewa karin ba zai shafi wadanda ba su samun wutar ta akalla sa’a 14 a rana ba.

Kamfanin raba wutar lantarki na  Kaduna (K-power) ya tabbatar da yin karin farashin a wata sanarwa da ya fitar.

A cewar kamfanin, “Daga ranar Talata, 1 ga watan Satumbar 2020, sabon karin kudin wuta zai fara aiki.

“Abokan huldarmu da ke rukunin D da E, karin bai shafe su ba, amma na rukunin A kuwa farashin ya tashi daga N40 a kan kowane Kilowatt da suke biya a baya zuwa N56.31.

“Wannan karin ya shafi watannin Satumba zuwa Disambar 2020 ne kawai,” inji sanarwar.

Shi ma kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na shiyyar Legas da ke Ikeja ya tabbatar da karin, ko da yake ya ce kawo yanzu bai shafi abokan huldarsa da ke samun wuta kasa da sa’a 12 ba, har sai zuwa lokacin da aka inganta ta.

Aminiya ta gano cewa a ranar Litinin kamfanoni uku suka mika rahoton ci gaban samuwar wutar ga NERC, ta kuma amince musu da su yi karin, yayin da ragowar ke jiran yin haka zuwa karshen wannan watan.