✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kara gishiri a maganar kudadena —Abdulaziz Yari

’Yan siyasa sun mayar da miliyan N278 kotu ta kwace Dala miliyan 621

Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Abdulaziz Abubakar Yari ya musanat labarin da ke cewa kotu ta umarci a kwace kudinsa Dala milliyan 621.

Da yake karin haske kan hukuncin da kotun ta yanke kan wasu kudade da ake tuhumar tsohon gwamnan, kakakinsa, Abdulrahaman Yahaya, ya ce Naira milliyan 278 ne kotu ta umarci a rufe a asusun tsohon gwamnan a bankunan Polaris da Zenith.

Ya ce babu gaskiya a labarin da ke yawo a wasu kafafen yada labarai cewa Dalar Amurka milliyan 621 kotu ta kwace a hannun tsohon gwamnan, sannan ya bukaci kafafen yada labarai su rika tantance labari kafin su yada domin guje wa kowa rudani.

Abdulrahaman ya zargi ’yan sisyasa da kokarain bata wa tsohon gwaman suna domin samun wata kujerar siyasa.

Don haka ya yi kira ga ’yan jarida su giju biye wa ’yan sisaya da ke neman amfani da su wajen bata sunan wani don biyan bukatu na siyasa.

Hadimin tsohon gwamna ya ce Yari ya rike manyan mukamai da dama kafin zamansa gwamna, amma iya kudin da aka samu a asusun ajiyarsa su ne miliyan N278.

A cewarsa, wannan ya nuna cewar Yari mutum ne mai kishin kasa da son al’ummarsa.

Hukuncin kotu

Aminiya ta kawo muku rahoton yadda Babban Kotun Tarayya da ke zamanta a Gusau ta ba da umarnin kwace kudaden tsohon gwamnan ne saboda ya kasa cikakken bayanin yadda ya same su.

Alkalin Kotun, Mai Shari’a Ijeoma Ojukwu ta yanke hukuncin ne a ranar Talata 26 ga Janairu 2021, yayin sauraron  shari’ar da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da Laifukan Zamba (ICPC) ta gurfanar da tsohon gwamnan.

ICPC ta kai shigar da karar ce tana bukatar a mallaka wa Gwamnatin Tarayya kudaden da ta gano a wurin tsohon Gwamnan Jihar Zamfara daga 2011 zuwa 2019 wanda Hukumar take bincike a kansa.

Hukumar ta yi karar sa ne tare da kamfanoninsa biyu; Kayatawa Nigeria Ltd da kuma B. T. Oil and Gas Nigeria Ltd bisa zargin kudaden an same su ne ta haramtacciyar hanya.

Kudaden da kotu ta kwace

Kudaden da Babbar Kotun Tarayya ta ba da umarnin kwacewan sun hada da Dala 613,192.49 da kuma Naira miliyan 24.3 a asusun ajiyar Abdulaziz Yari daban-daban a Bankin Zenith.

Kotun da ke zamanta a Gusau ta kuma kwace Dala 56,056 da ke asusun ajiyar tsohon gwamnan a Bankin Polaris duk ta mallaka wa Gwamnatin Tarayya.

A watan Agustan 2019 Mai Shari’a Taiwo Taiwo ya ba da umarnin wucin gadi na mallaka wa Gwamnatin Tarayya kudaden bisa kamar yadda lauyan ICPC, Osuobeni Akponimisingha ya bukata.

A lokacin Mai Shari’a Taiwo ya bukaci Hukumar ta wallafa a manyan jaridu guda biyu, idan akwai wani da ke kalubalantar a kwace kudaden a mallaka su ga Gwamantin Tarayya.