✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kara gwangwaje dan sandan da ya ki karbar rashawar $200,000

An kara yi wa Daniel Itse Amah karin girma zuwa Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda da kuma kyautar Naira miliyan daya.

Hukumar Kula da Aikin Dan Sanda ta Najeriya ta kara daga matsayin dan sandan nan da ya ki karbar cin hancin Dala 200,000 zuwa Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda da kuma kyautar Naira miliyan daya.

Bayan karin girma da aka yi masa daga matsayin DSP zuwa CSP wata biyu da suka gabata, a ranar Alhamis Shugabar Hukumar, Mai Shari’a Clara Ogunbiyi, ta sanar cewa ya cancanci fiye da haka domin kara zaburar da takwarorinsa, inda ta sake daga likafarsa zuwa matsayin DCP.

“Dokar da ta kafa wannan hukuma ta ba mu izinin karrama ’yan sandan da suka nuna bajinta ta hanyar kara musu girma.

“Don haka ina sanar da karin girman CSP Daniel Amah zuwa matsayin Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda (DCP),” in ji Mai Shari’a Ogunbiyi.

Dan sanda mai suna Daniel Amah wanda DPO ne a yankin Nasarawa a Jihar Kano, Amah, ya yi watsi ne da cin hancin Dala dubu 200 da wasu ’yan fashi suka yi mishi tayi.

A ranar 4 ga watan Oktoba, 2022 Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya karrama DPO Daniel Itse Amah da kyautar rikon amana, a lokacin Babban Taron Yaki da Rashawa karo na Hudu, wanda Hukumar Yaki da Rashawa (ICPC) ta shirya.

Daga baya hukumomi daban-daban sun yi ta karrama dan sandan bisa rikon amanarsa.

Makusantan dan sandan da a baya suka rika yi masa shagube, sun dawo suna masa murna bayan sun ga irin karramawar da gwamnati ta yi masa.