✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kara kudin wutar lantarki da kaso 75 a Sri Lanka

Karin zai fara aiki ne ranar 10 ga watan Agusta

Hukumar da ke kula da wutar lantarki ta kasar Sri Lanka, a ranar Talata ta sanar da yin karin farashin wutar da kaso 75 cikin 100.

Shugaban Hukumar Kula da Kadarorin Gwamnati ta kasar, Janaka Ratnayake, wanda ya sanar da hakan ya ce karin zai fara aiki ne daga ranar 10 ga watan Agustan 2022.

Da wannan sabon karin dai, wadanda suke shan wutar da adadinta ya kai kamar awo 30 za su sami karin kudin da suka kai kimanin Rufi (kudin Indiya) 198, yayin da masu shan awo din da ya kai 60 a yanzu za su sami karin Rufi kusan 200.

Hukumar lantarkin kasar dai tun farko ta nemi karin farashin ne da kaso 276 ga kwastotomin da ke shan sama da awo 90, amma aka amince da karin kaso 125 cikin 100.

Karin dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ta fada matsin tattalin arziki mafi muni a tarihinta tun bayan samun ’yancin kanta.

Ko a watan da ya gabata dai sai da tsananin zanga-zangar da mutanen kasar ke yi ta yi sanadin tsohon Shugaban Kasar, Gobataya Rajapaksa, ya sauka daga mukaminsa bayan ys tsere daga kasar.