✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kara lokacin rajisatar lambar dan kasa da layin waya

An yi karin lokaci zuwa ranar 9 ga watan Fabrairu, 2021 ga marasa lambar NIN

Gwamnatin Tarayya ta tsawaita wa’adin da ta bayar na yi wa layukan waya rajista da lambar shaidar dan kasa (NIN).

Bayan wani taron masu ruwa da tsaki a ranar Litinin, Ma’aikatar Sadarwar da Tattalin Arziki na Zamani ta ce a kara sati uku a kan wa’adin da ta bayar na 30 ga watan Disamba, 2020 a karon farko.

Mataimakin Shugaban Hukumar NCC mai kula da sadarwa, Umar Danbatta, da Shugaban Hukumar Shaidar Dan Kasa (NIMC), Umar Aziz, ne suka sanar da hakan a cikin sanarwar.

“An cimma wadannan matsaya bisa amincewar Gwamnatin Tarayya:

“Karin sati uku ga masu layukan waya da ke da lambar NIN daga ranar 30 ga Disamba, 2020 zuwa 19 ga Janairu, 2021;

“Karin sati shigda ga masu layukan waya marasa lambar NIN daga 30 ga Disamba, 2020 zuwa 9 gwa Fabrairu, 2021.

“NIMC ta kuma bullo da hanyoyin yi wa ’yan Najeriya rajista cikin kiyama matakan kariyar COVID-19, musamman sanya takunkumi da kuma bayar da tazara,” inji sanarwar.