✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kara yi wa Buhari rigakafin Coronavirus karo na uku

Mutuwar mutum 8 daga cikin kowane 10 na da nasaba ne da rashin karbar rigakafin.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya karbi allurar rigakafin Coronavirus samfurin Pfizer karo na uku a ranar Talata.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ta shiga zayaye na hudu na annobar Coronavirus yayin da aka samu karin kashi 500 bisa 100 na masu kamuwa da cutar a tsawon makonni biyu da suka gabata.

Likitan Shugaba Buhari, Dokta Suhayb Rafindadi ne ya yi masa allurar a fadarsa da ke Abuja

Da yake jawabi a kan lamarin, Dokta Faisal Shuaib, Shugaban Hukumar Lafiya a Matakin Farko ta Najeriya (NPHCDA), ya ce karbar rigakafin da Shugaba Buhari ya yi ya sake tabbatar da muhimmancinta ga ’yan kasa.

Shugaba Buhari rika da katin shaidar karbar rigakafin Coronavirus.
Shugaba Buhari a lokacin da yake karbar rigakafin a karo na uku

Dokta Faisal ya ce binciken da suka gudanar ya gano cewa daga cikin kowane mutum goma da cutar Coronavirus ta yi sanadiyar ajalinsu, mutum takwas daga ciki mutuwarsu na da nasaba ne da rashin karbar rigakafin.

A wannan wata na Disamba ne Hukumar NPHCDA ta ce za ta fara jaddada wa ’yan kasar karbar rigakafin a karo na uku ga wadanda suka yi a matakin farko.

Bayanan da Hukumar Yaki da Cututtuka masu Yaduwa a Najeriya NCDC ta fitar sun nuna cewa, Najeriya ta fuskanci karuwar masu kamuwa da cutar Coronavirus ninki biyar cikin mako biyu da suka wuce a yayin da aka samu bullar sabon nau’in cutar da ake kira Omicron.