✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An karrama dan sandan da ya ki karbar cin hancin $200,000 a Kano

An dai ba shi kyautar girmamawa ne a Kano

Babban Sufeton ’Yan Sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya ba SP Daniel Itse Amah, dan sandan da ya ki karbar cin hancin Dalar Amurka 200,000 kyautar grimamawa.

Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda, DCP Abubakar Zubair, ne ya gabatar masa da kyautar a hedkwatar rundunar da ke Kano ranar Litinin a madadin Babban Sufeton.

Idan za a iya tunawa, dan sandan ya jagoranci kama wani mai suna Ali Zaki tare da wasu ’yan sanda kan zargin wani fashi da makami na sama da Naira miliyan 320.

Sai dai a kokarin yin rufa-rufa a kan zargin, babban wanda ake zargin ya yi tayin ba dan sandan cin hancin kudaden, amma ya ki karba.

A cewar DCP Abubakar, Babban Sufeton ya jinjina wa jami’in saboda nuna halin dattaku da kwarewa a aiki.

Ya ce. “Muna gabatar da wannan kyautar girmamawar ga SP Daniel Itse Amah saboda nuna nagartar da ba a cika samu ba a aikinsa.

“An karrama shi saboda yadda ya jagoranci kama Ali Zaki da wasu ’yan sanda kan batun wani fashi da makami na Naira miliyan 320 da dubu 500, inda aka ba shi toshiyar bakin Dalar Amurka 200,000, amma ya ki karba.”