✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe basarake mako daya bayan garkuwa da shi a Neja

Tun da farko dai sai da ’yan bindigar suka nemi N800,000 a matsayin kudin fansar sa.

Mako daya bayan ’yan bindiga sun yi garkuwa da shi, rahotanni sun tabbatar da kisan Dagacin garin Madaka da ke Karamar Hukumar Rafi ta Jihar Neja, Zakari Idris.

A ranar Lahadin da ta gabata ne ’yan bindiga kusan su 50 suka yi wa garin kawanya tare da kashe mutum uku da kuma sace basaraken a karo na biyu.

Shugaban Ma’aikatan Shugaban Karamar Hukumar ta Rafi, Mohammed Mohammed shi ne ya tabbatar da kisan a zantawarsa da Aminiya ta wayar salula.

Ya ce tun da farko  sai da ’yan bindigar suka tuntubi iyalan marigayin tare da neman N800,000 a matsayin kudin fansa.

Mohammed ya ce mutum biyar da aka sace tare da shi wadanda su suka biya kudin fansarsu sun tabbatar da cewa ’yan bindigar sun kashe basaraken.

A cewarsa, mutanen sun ce ya rasu ne sakamakon irin azabar da ya sha a hannun masu garkuwar saboda irin dukan da suka rika yi masa ba kakkautawa.

Mohammed ya kuma ce ’yan bindigar sun binne gawar mamacin a daji bayan kashe shi.

An sace Mai garin na Madaka ne a karo na biyu kimanin wata daya bayan sako shi, inda a wancan karon ya shafe wata uku a hannun masu garkuwar.

Yayin ba-ta-kashin da aka yi kafin sace Dagacin a ranar Lahadi, an kashe shugaban kato-da-gora na garin, Isyaku Alhassan, dansa, Abdulhamid da kuma wani mutum daya.

Kazalika, an jikkata wasu mutanen da dama tare da kone gidaje masu yawa a garin.