✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan banga ya rasu yayin artabu da ’yan bindiga

Ana cikin ruwan sama aka gwabza yaki tsakanin ’yan banga da ’yan bindiga.

Wani dan banga ya rasu a yayin artabu da ’yan bindiga a yankin Agbudu na Karamar Hukumar Koton-Karfe, Jihar Kogi.

Wani daga cikin ’yan bangar ya ce lamarin ya faru ne bayan sun gano maboyar wasu ’yan bindiga a wani daji da ke yankin na Agbudu.

  1. Ya dawo gida bayan bacewarsa da shekara 65
  2. ’Yar shekara 37 ta haifi jarirai 10 lokaci guda

“Al’amarin ya faru da yammacin ranar Talata yayin da ake tsaka da ruwa; Mun tsaya don mu fake, a nan ne muka gano wata maboyar ’yan bindiga,” inji dan bangar da ya nemi a boye sunansa.

Ya kara da cewa ’yan bindigar na hangen su sai suka fara harbi, a lokaci ne daya daga cikinsu ya kwanta dama.

Ya kara da cewa, “Muna tsaka da artabu da ’yan bindigar ba mu yi aune ba wani daga cikinsu ya zo ta bayanmu ya harbi daya daga cikinmu.”

Ya ce Shugaban Karamar Hukumar Koton-Karfe, Isah Abdulkarim na da masaniyar faruwar lamarin.

Tuni aka binne dan bangar da ya rasu, mai suna Awwalu Mohammed, wanda dan asalin kauyen Tanahu ne a jihar.

Kakakin ’yan sandan jihar Kogi, ASP Oyye Aya, bai amsa kiran wayarmu ko rubutaccen sakon da muka aike masa ba kan lamarin.