✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kashe dan bindiga an cafke wasu 8 a Zamfara

’Yan sanda sun kwato kudin fansa da ’yan bindiga da kuma makamai a hannun wadanda aka kama

An kashe wani dan bindiga a yayin da wasu mutum takwas suka shiga hannun jami’an tsaro a Jihar Zamfara.

Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar, Muhammad Useini Gumel, ya ce an kwace Naira miliyan 2.5 da aka ba wa ’yan bindiga kudin fansa da kuma makamai da motocin sata a hannun wadanda aka kama.

Ya bayyana cewa a cikin mutum takwas din da aka kama akwai ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane da ’yan fashi da kuma masu kwacen mota.

A cewarsa, harkokin yau da kullum na ci gaba da kankama a jihar, a yayin da rundunarsa take samun nasarori a samamen da take kaiwa a wurare masu hadari da maboyan bata-gari da nufin murkushe su a jihar.

Duk da haka ya yi kira ga al’ummar Jihar Zamfara da su rika taimaka wa ’yan snada da bayanai kan motsin bata-gari, yana mai ba su tabbacin samun cikakkiyar kariya da kare sirri.