✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe dillalin shanu saboda ya ki sayen na sata

Mahara sun kashe dillali saboda kin sayen shanun sata

Mahara sun bindige wani sannanen dillalin shanu a  Sabon Garin Tabkin Kazai da ke Karamar Hukumar Tsafe a Jihar Zamfara  saboda kin amincewarsa ya siyan shanun da aka sato.

Mazauna sun shaida wa Aminiya cewa, ’yan bindigar da suka yi wa garin shigar bazata, kai tsaye suka nufi wurin dillalin shanun mai suna Alhaji Audu Mai Sayen Shanu, wanda aka fi sani da Audu na ’Yar yaye kuma suka harbe shi nan take sannan suka arce.

Sun ce, “Alhaji Audu ya shahara sosai a Gabashin Karamar Hukumar Tsafe kuma a hakikanin gaskiya ba ya da na daya a wajen sayen shanu.

“A baya kusan sau uku mahara dauke da makamai ke shigowa garinmu su yi awon gaba da dabbobi.

“Sau da yawa sun saba kawo masa shanun sata amma sai ya ki amincewa tare da yin watsi da bukatarsu ta neman kulla wata alaka ta kasuwanci da su.”

“Ya rika shaida masu cewa tun da dadewa ya daina harkar shanu bayan ya fahimci cewa shanun sata sun mamaye kasuwanni da dama a wannan shekara.

“Bayan da suka kashe shi sun kama gabansu ba tare da karbar ko sule a hannunsa ba kuma galibin mazauna garin ba su da masaniyar an kashe shi saboda shi kadai suka yi wa takakkiya,” a cewa wani mazauni.

Ya zuwa tattara wannan rahoto, babu wani bayani da ya fito daga Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Zamfara dangane da lamarin kuma duk wani kokari da Aminiya ta yi na tuntubar kakakin rundunar, SP Muhammad Shehu, ya ci tura.