✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kashe fararen hula sama da 300,000 a rikicin Siriya — Rahoto

Rahoton ya ce adadin bai ma shafi sojoji da mayaka ba

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya ce fararen hula sama da 300,000 ne aka kashe a shekaru goman farko na rikicin kasar Siriya.

Haka nan, majalisar ta ce an kashe sama da mutum 100 da ake tsare da su a sansanin kasar.

Ofishin Kare Hakkin Dan Adam na Majalisar ya ce ya wallafa rahoton kashe fararen hular ne bayan bincike da kididdigar da majalisar ta yi kan wadanda suka rasa rayukansu a rikicin kasar.

Kamar yadda rohoton ya nuna, a kiyasce, fararen hula 306,887 ne aka kashe a rikicin Siriya tsakanin daya ga Maris, 2011 zuwa 31 ga Maris, 2021.

Babban Jami’i a Majalisar, Michelle Bachelet ya ce, “Kashe fararen hula 306,887 da aka yi zai yi tasiri ainun ga ahalin mamatan da ma al’ummarsu.”

Majalisar ta kara da cewa, wadannan alkaluma da aka fitar ba su shafi sojoji da kuma mayakan da aka kashe a rikicin kasar ba, haka ma ba su hada da mutanen da ’yan uwansu suka kashe su suka binne ba tare da sanar da hukumomi ba.

Rikicin Siriya ya soma ne a watan Maris na 2011 biyo bayan zanga-zangar kin jinin gwamnati da ’yan kasar suka gudanar a sassa daban-daban inda suka bukaci a inganta tsarin Dimokuradiyyar kasar.