✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sumoga sun kashe jami’in Kwastam a Kwara

Wasu da ake zargin ’yan fasa-kwauri ne sun kashe wani jami’in Kwastam a Juma’ar da ta gabata a lokacin da suke sintiri a hanyar Sinau…

Wasu da ake zargin ’yan fasa-kwauri ne sun kashe wani jami’in Kwastam a Juma’ar da ta gabata a lokacin da suke sintiri a hanyar Sinau zuwa Kenu da ke Igboho cikin Karamar Hukumar Baruteen, Jihar Kwara.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin ranar Litinin a Ilorin babban birnin jihar, mai magana da yawun hukumar, Mista Chado Zakari ya ce, tun farko jami’an sun kama buhun shinkafa 40 da jarkokin fetur 30 da aka yi fasa-kwaurinsu aka boye a dajin hanyar Sinau zuwa Kenu.

Ya ce wadanda ake zargin sun bude wa jami’an wuta ne a daidai lokacin da suke kokarin kwashe kayan da aka gano zuwa ma’ajiyar gwamnati.

Ya kara da cewa, sakamakon musayar wutar da aka yi tsakanin jami’ansu da bata-garin, sun rasa mutum daya sannan uku sun ji rauni wanda a yanzu haka ana ci gaba da yi musu magani.

Zakari ya ce tuni an yi wa marigayin, Mista Saheed Aweda jana’iza kamar yadda Musulunci ya tanadar a mahaifarsa Popogbona da ke Karamar Hukumar Ilorin ta Yamma a jihar.

Ya ce sun soma bincike don kamo bata-garin duk inda suka shiga don su fuskanci hukunci daidai da laifin da suka aikata.