✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kashe kasurgumin dan daba

Wani rikici ya yi ajalin wani rikakken dan daba Abiola Ebila, wanda aka fi sani da Eibla a garin Ibadan na jihar Oyo. Kakakin Rundunar…

Wani rikici ya yi ajalin wani rikakken dan daba Abiola Ebila, wanda aka fi sani da Eibla a garin Ibadan na jihar Oyo.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Oyo Olugbenga Fadeyi ya ce rikicin ya barke ne a a yankin Kutedia ranar Lahadi.

Jami’in ya ce tuni aka tura jami’an rundunar domin kwantar da rikicin, sai dai zuwa lokacin hada rahotonmu ya ce ba shi da cikakken bayanin abin da ya haddasa rikicin da ya yi sanadiyyar kashe Ebila.

A cikin watan Mayu zugar Eibla, wadda ta yi kaurin suna a garin Ibadan ta kashe shugaban kungiyar ‘yan daba ta Mosood Oladokun wadda aka fi sani da “Ekugbemi”.

Rahotanni sun ce bayan barkewar rikicin ’yan dabar na ranar Lahadi ne jami’an tsaro suka kai dauki a yankin, lamarin da ya yi sanadiyyar kashe Ebila.