✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe ladani yana cikin kiran sallah a Zamfara

Ladanin yana tsaka da kiran sallah ’yan bindiga suka shiga masallacin suka bude masa wuta

’Yan bindiga sun harbe wani ladani har lahira a lokacin da yake kiran sallah a garin Magazu da ke Karamar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara.

Mazauna garin sun shaida wa Aminiya cewa ladanin yana cikin kiran sallah a masallacin da ke kusa da gidansa ne ’yan bindigar suka shiga cikin masallacin suka bude masa wuta suka kashe shi nan take.

’Yan bindigar sun kuma nemi a biya su Naira miliyan a matsayin kudin fansar wani mutum da suka yi garkuwa da shi a lokacin harin na ranar Laraba a garin da ke kan hanyar Gusau zuwa Funtua.

Garin Magazu mai nisan kilomita 40 daga Gusau, fadar gwamantin Zamfara, ya fara fama da harin ’yan bindiga ne bayan an tsinci gawar wani dan bindiga a kusa da garin.

Tun daga lokacin ’yan bindigar suka lashi takobin daukar fansa, inda suke zargin mutanen garin ne suka kashe dan bindigar.

Amma wani dan garin ya ce, “Ba mu muka kashe musu dan uwa ba.”

Wakilinmu ya gano cewa a halin yanzu ’yan bindiga sun matsa wa garin lamba, duk da cewa akwai jami’an tsaron da ke aiki a garin.

’Yan sanda ba su ce komai ba game da harin har zuwa lokacin da muka kammala hada wannan rahoton.