✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kashe likitan Birtaniya da ya je aikin ceto a Ukraine

Wani dan kasar Birtaniya da ya je Ukraine ba da gudmmawar ceto rayuwar mutanen da yakin kasar da Rasha ya rutsa da su mai suna…

Wani dan kasar Birtaniya da ya je Ukraine ba da gudmmawar ceto rayuwar mutanen da yakin kasar da Rasha ya rutsa da su mai suna Craig Mackintosh, ya mutu.

Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar ce ta bayyana hakan a safiyar Alhamis, inda ta ce tuni ’yar uwar margayin ta assasa asusun bada tallafin jana’izarsa ta intanet.

“Dan uwanmu ya sadaukar da rayuwarsa domin ceto wadanda yaki ya rusta da su a Ukraine, kuma hakan ya yi sanadiyar rasa rayuwarsa.

“Baya ga haka, gawarsa ta makale a mutuwaren Ukraine din kuma ana bukatar tallafin Dala 5,222 domin dawo da shi gida a binne shi,” in ji sakon da ’yar tasa ta wallafa.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton dai, an samu kusan rubi biyu na kudin da ’yar uwar margayin ta ambata.

Tuni dai Ofishin Raya Kasashen Commonwealth, ya sanar cewa zai tallafa wa dangin Mackintosh, da ke yankin Norfolk a yankin Gabashin kasar Ingila.