✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kashe mai tabin hankali ‘bisa kuskure’ kan zargin satar yara

An kashe shi ne lokacin da yake tare da ’yar cikinsa

Mutanen gari sun kashe wani mai fama da tabin hankali a unguwar Hayin Nasara da ke Suleja a jihar Neja bisa kuskure, bayan sun zarge shi da zama barawon yara.

Aminiya ga gano cewa mutumin, mai suna Nasiru Mustapha, ya gamu da iftila’in ne ranar Lahadi.

Daya daga cikin makwabtan marigayin, Ibrahim Ahmad, ya ce mutumin bai dade da tarewa a yankin ba, bayan tasowarsa daga Gidan Busa da ke Katari a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna, saboda matsalar tsaro.

Ibrahim ya ce marigayin na kula da wani rumbun sayar da hatsi ne, kafin daga bisani ya hadu da larurar tabin hankalin, wacce ta sa aka yanke shawarar mayar da shi da matarsa da kuma dansu zuwa can Katarin, bayan ingantuwar al’amuran tsaro a yankin da ya fito.

Ya ce ranar da lamarin zai faru, Nasiru na rike da daya daga cikin ’ya’yansa mata ne a hanyarsu ta tafiya garin nasu, sai kawai mutane suka tare shi suka ce sato ta ya yi.

Ibrahim ya kuma ce, “Matar da Nasirun yake haya a gidanta ta yi kokarin saka baki, amma mutanen suka yi mata ca a ka, kafin ta samu ta gudu ita ma. Suna zarginta da ba barawon yara mafaka.

Da wakilinmu ya tuntubi Baturen ’Yan Sanda (DPO) na yankin Sabon Wuse, CSP Lateef Biodun, ya tabbatar da faruwar lamarin.

DPOn ya kuma ce tuni suka gano mutanen da ke da hannu a lamarin, wadanda suka riga suka cika wandonsu da iska, inda ya ce suna nan suna kokarin ganin sun kama su.