✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe makiyaya 6 a Taraba —’Yan sanda

Mutanen kauyen sun aiwatar da ramuwar gayya a kan Fulanin.

Rundunar ’Yan Sandan  Jihar Taraba ta sanar da cewa wasu Fulani makiyaya shida sun yi gamo da karshensu a hannu mazauna wani kauye da ke jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar, ASP Abdullahi Usman  ya shaida wa Aminiya cewa Fulani shida da aka kashe sun hada da yara maza hudu da mata biyu.

  1. Mutum 5 sun mutu bayan fashewar bam a Jamus
  2. Ango ya fasa auren amayarsa a kan naman tunkiya

Ya ce an kashe su ne a wani hari da aka kai a kauyen Mungadoso da ke Karamar Hukumar Karim-Lamido ta jihar a ranar Litinin.

Usman ya bayyana cewa,  al’ummar Mungadoso ne suka kai wa Fulanin hari biyo bayan samun gawar na wani mutumin kauyensu da ya bace kwanaki biyu da suka gabata.

Mazauna kauyen Mungadoso sun yi zargin cewa Fulani makiyaya ne suka kashe mutumin, lamarin da ya kai su ga aiwatar da ramuwar gayya a kan Fulanin.

Ya ce, wasu Fulani guda hudu daga yankin sun bata kuma ’yan sanda da ’yan banga suna cikin daji suna nemansu.

Kazalika, ya kara da cewa tuni al’amura suka koma daidai a kauyen Mungadoso, bayan tashin-tashina da aka samu.