✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe makiyayi a harin daukar fansa a Kaduna

Kwana biyu ke nan bayan harin da aka kashe manoma da dama a yankin.

A wani harin kwanton bauna da ake ganin na daukar fansa ne, wadansu mutane sun kashe wani makiyayi a kauyen Goska da ke yankin Kaninkon a Karamar Hukumar Jema’a ta Jihar Kaduna.

Lamarin na zuwa ne kwana biyu bayan kashe manoma da dama a yankin.

An dai nemi matashin makiyayin mai suna Hamisu Bello an rasa ne bayan ya fita kiwo bai dawo ba, daga bisani aka tsinci gawarsa a daidai Rafin Dadi da ke Masarautar ta Kaninkon da saran adduna a jikinsa.

Rundunar musamman ta OPSH da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Kudancin Kaduna, ta tabbatar da kisan a rahotonta ga Gwamnatin Jihar Kaduna.

Cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, Kwamishinan Tsaro da Al’amuran Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan ya ce an gano gawar makiyayin ne bayan fadada bincike.

“Binciken da sojoji suka gudanar ya tabbatar da cewa wadansu fusatattun ’yan yankin ne suka kashe shi bayan harin da aka kai musu inda aka kashe manoma hudu,” inji sanarwar.

Ya ce Gwamnan Jihar, Nasir Ahmed El-Rufai ya yi Allah wadai da kisan, inda ya gargadi mutane da su guji daukar doka a hannu ko su gamu da fushin hukuma.

Aminiya ta ruwaito cewa a yammacin ranar Litinin ne wadansu mahara suka kai hari a wata gona a kauyen na Goska suka kashe mutum biyar tare da jikkata wadansu biyu.

Hudu daga cikin wadanda aka kashen sun mutu nan take, daga baya na biyar  din ya cika a Babban Asibitin Kafanchan.