✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe malami da dalibi a wata Kwaleji a Legas

A halin yanzu dai ana cikin zaman dar-dar a kwalejin da kewayenta.

An kashe wani malami da dalibi a Kwalejin Horas da Ayyukan Kula da Lafiya a matakin farko ta Michael Otedola (MOCPED) da ke Jihar  Legas.

Aminiya ta ruwaito cewa an kashe malamin mai suna Ahmed Saheed a kusa da garin Poka yayin da shi kuma da kuma dalibin mai suna Razak Bakare aka kashe shi a harabar makarantar wanda duk suke yankin Karamar Hukumar Epe a Jihar Legas.

Wata majiya ta ’Yan sanda da ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce duka kisan guda biyu an yi su ne a lokuta daban-daban amma tsirarsu ba ta wuce sa’o’i 48 ba.

Majiyar ta ce dalibin wanda bincike ya nuna an rika fakonsa shi aka fara kashewa a ranar Laraba sannan aka kashe malamin a ranar Juma’a.

Rahotanni sun ce a halin yanzu dai ana cikin zaman dar-dar a gaba daya yankin na Poka da kwalejin take sakamakon yanayin da mutane suka tsinci kawunansu saboda aukuwar lamuran.

Oba Babatunde Ogunlaja, wani basarake a yankin, da yake bayyana takaicinsa ya ce wannan al’amari ya ruguza zaman lafiya da kwanciyar hankali da suka saba da shi a garin Noforija

A kan haka ne ya yi kira ga mahukuntan kwalejin da su dasa na’urori masu daukar hoton bidiyo na CCTV a ciki da kewayen makarantar.

Ogunlaja ya kuma nemi Gwamna Babajide Sanwo-Olu da Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Legas, Hakeem Odumosu, da jibge karin jamian tsaro a yankin.

Kazalika, ya nemi Gwamnatin Jihar Legas ta sake gina katangar kwalejin da ta dauki tsawon lokaci da faduwa.