✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe mana sojoji 498 a Ukraine —Rasha

Sojoji dubu 1 da 597 da sun samu raunuka a yakin.

A karon farko mahukuntan Rasha sun tabbatar da cewa sojojin kasar 498 ne suka halaka tun bayan kaddamar da kutse a kan Ukraine bisa umurnin Shugaba Vladimir Putin na Rasha.

Mai Magana da yawun Ma’aikatar Tsaron Rasha, Igor Konashenkov ya ce, baya ga sojojinsu 498 da suka mutu a fagen-daga, har ila yau akwai karin sojoji 1,597 da suka jikata sakamakon wannan yakin da suke yi da Ukraine.

Wannan na zuwa ne bayan wata sanarwa da Ukraine ta fitar, inda ta yi ikirarin cewa, Rasha ta yi asarar sojojin da yawunsu ya zarta dubu 5 da 700, sannan ta ce, ta kuma  kama kimanin sojojin Rasha 200 a matsayin fursunonin yaki.

Haka kuma ita ma Rashan ta yi ikirarin kashe sojojin Ukraine sama da 2,870 kuma kusan 3,700 suka jikkata.

A can baya dai, gwamnatin Rasha ta gasgata cewa, lallai ta yi asarar wasu sojojinta, amma ba ta bayar da alkalumansu ba, sai a wannan karo.

Wannan sanarwa da Ma’aikatar Tsaron Rashan ta fitar na zuwa ne bayan mako guda da shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi shelar kaddamar da luguden wuta akan makwabciyarsu Ukraine.

A bangare guda, kungiyoyi masu zaman kansu a Rasha sun ce,  gwamnatin ta Rasha ta tilasta wa wasu mutane shiga cikin wannan yakin bayan ta yi musu rajistan dole a matsayin sabbin sojojin kasar, amma Ma’aikatar Tsaron kasar ta ce, sam al’amarin ba haka yake ba.

Rasha dai ta ce, sojojinta na ci gaba da aiki tukuru domin ganin sun kakkabe akidar ‘yan Nazi daga zukatan ‘yan Ukraine.

Ukraine ta ce, sama da fararen hularta 350 ne aka kashe tu bayan fara yakin a ranar Alhamis da ta gabata.