✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kashe masu garkuwa a wurin karbar kudin fansa

’Yan banga sun kashe su gaba daya suka kubutar da wanda aka sace.

Wasu gawurtattun ’yan bindiga sun gamu da ajalinsu a lokacin da suka je karbar kudin fansa daga iyalan wani dattijo da suka yi garkuwa da shi a Jihar Taraba.

’Yan banga ne suka bindige ’yan bindigar da suka hana yankin Karamar Hukumar Gassol ta Jihar sakat, a garin Sabongida lokacin da suka je karbar kudin fansa da suka bukata daga iyalan dattijon.

Bayan ’yan bindigar da ake kira Sani da Musu sun yi garkuwa da mutumin ne suka kuma umarci iyalansa su kai musu kudin fansa Naira dubu dari uku a wani wuri da suka ayyana a garin Sabongida.

Ana cikin haka ne ’yan bangar suka samu labari, inda suka yi hanzari suka je suka yi wa ’yan bindigar kwanton bauna a wurin.

SAURARI: Muhimmancin shayar da yara non uwa:

Bayan dan lokaci ’yan bangar suna labe a wurin sai ga masu garkuwar, kowannensu dauke da bindiga kirar AK 47, sun taso keyar dattijon zuwa wurin, ba su san da tarkon da ’yan bindigar suka shirya musu ba.

Sai da ’yan bangar suka bari su biyun sun je har sun duka za su dauki kudin fansar ke nan, sai ’yan bangar suka bude musu wuta, nan take suka kashe su, suka kuma kubutar da dattijon suka kwace bindigogin masu garkuwar.

Majiyarmu a garin ta ce gungun ’yan bindigar Sani da Musa da yaransu sun yi shekaru suna ta kashe mutane a yankunan Borno-Korokoro da Tella da Sabongida da Dananacha da wasu garuruwa da kauyuka da ke kan babbar hanyar Jalingo zuwa Wukari.

Mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sandan Jihar Taraba, ASP Abdullah Usman ya tabbatar da kashe ’yan bindigar.