An kashe matashi saboda budurwa a Kaduna | Aminiya

An kashe matashi saboda budurwa a Kaduna

‘Yan sanda
‘Yan sanda
    Mohammed I. Yaba, Kaduna da Abubakar Muhammad Usman

An samu rudani a yankin Tudun Wada da ke Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu a Jihar Kaduna, bayan da aka kashe wani matashi sakamakon sabani da ya samu da wata budurwa.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 4:00 na yammacin Lahadi a unguwar Kaltungo.

Aminiya ta gano cewar matashin da budurwar na da alaka ta ‘yan uwantaka a tsakaninsu, amma sabani ya shiga har ta kai ga matashin ya mare ta a fuska.

Hakan ya sanya ta fusata tare da gayyato saurayinta da abokansa inda suka yi masa dukan kawo wuka, sannan suka daba masa wuka a wuya da kuma kirjinsa.

Wata majiya a yankin ta shaida wa Aminiya cewar an daba wa matashin wuka kuma daga bisani rai ya yi halinsa.

Kazalika, majiyar ta ce budurwar da saurayin nata tare da abokansa sun tsere sun bar matashin cikin jini a kwance.

Sai dai lokacin da wasu matasan yankin suka kai dauki wajen da lamarin ya faru don kai wa matashin dauki sun samu gawarsa kwance cikin jini, sannan sun iske makamai a ko ina a wurin da lamarin ya faru.

Amma daga bisani jami’an ‘yan sanda sun isa yankin don gudanar da bincike.

Mun yi kokarin jin ta bakin kakakin ‘yan sandan Jihar, DSP Mohammed Jalige kan lamarin amma bai amsa wayar da aka yi masa ba.

Tuni aka birne gawar matashin kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.