✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe mutum 15 a Taraba —’Yan sanda

Rundunar ‘yan sanda a jihar Taraba ta ce an kashe mutane 15 a wani fadan kabilanci tsakanin ‘yan kabilar Shomo da Jole a karamar hukumar…

Rundunar ‘yan sanda a jihar Taraba ta ce an kashe mutane 15 a wani fadan kabilanci tsakanin ‘yan kabilar Shomo da Jole a karamar hukumar Lau.

Kakakin rundunar, DSP David Misal, ya shaida wa wakilin Aminiya cewa an kuma kone gidaje 100 a lokacin rikicin.

Binciken Aminiya ya gano cewa fadan ya barke ne a kan wani ruwa da ake kama kifi wanda kabilun biyu ke rigima a kan mallakarsa.

Taraba: Ana zaman zullumi a yankin Jukun

Coronavirus: Jama’a sun samu walwala a Jalingo

Rigingimu tsakanin kabilun biyu kan wannan ruwa sun jawo asarar rayuka masu yawan gaske.

Amma wata majiya ta shaida wa wakilin Aminiya cewa mutane 24 aka kashe a lokacin wannan mummunan fada.

Har yanzu kuma ba a gano wasu mutane masu yawan gaske da fadan ya rutsa da su ba.

Jihar ta Taraba dai na fama da rikice-rikicen kabilanci—ko a makon jiya ma sai da aka rasa rayuka a wani rikicin a tsakanin kabilun Tibi da Jukun.