✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kashe mutum 15 an yi garkuwa da 12 a Neja

Rahotanni sun ce wani dan sandan kwantar da tarzoma shima ya rasa ransa a harin.

Akalla mutum 15 aka tabbatar da mutuwarsu a garin Beri a yankin Bobi na Karamar Hukumar Mariga cikin Jihar Neja da safiyar Litinin.

Kazalika, wadansu mutum 12 sun samu raunuka yayin da wata kungiyar maharan ta daban ta yi garkuwa da wadansu mutum 12 a wani kauyen.

Rahotanni sun ce wani dan sandan kwantar da tarzoma shima ya rasa ransa a harin  da wasu ’yan bindiga suka kai a garin.

Sai dai rahotanni sun kuma ce ’yan bangar garin sun hallaka mahara biyar yayin farmakin.

Maharan sun kuma cinna wuta kan caji ofis na garin na Beri, lamarin da ya haddasa mutane da dama suka sami raunuka sakamakon turmutsitsin daga ya biyo bayan kona caji ofis din.  

A wani labarin kuma, wadansu maharan sun dira kan kauyen Garin-Gabas a ranar Litinin da safe amma sun gamu da turjiyar matasan.

Sai dai babu cikakkun bayanai dai game da adadin wadanda suka mutu ko suka jikkata a harin daga dukkanin bangarorin biyu.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, NISEMA, ta tabbatar da hare-haren amma ba ta yi karin haske a kai ba.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Wasiu Abiodun, bai amsa kiran da Aminiya ta yi masa ba domin jin ta bakin rundunarsa game da hare-haren.