✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe mutum 40 da Karamar Sallah a Taraba

Dan Majalisar Dattawa mai wakilta Taraba ta Kudu, Sanata Emmanuel Bwacha, ya ce ’yan ta’adda sun kashe sama da mutum 40 a lokacin hutun Ƙaramar…

Dan Majalisar Dattawa mai wakilta Taraba ta Kudu, Sanata Emmanuel Bwacha, ya ce ’yan ta’adda sun kashe sama da mutum 40 a lokacin hutun Ƙaramar Sallah a yankin.

Sanya Bwacha, wanda, ya ce maharan sun zo ne a kan babura suna yi wa mutane kisan gilla, har sojoji da sojoji da ’yan sanda da aka girke domin kare al’umma ba su bari ba.

Ya jajanta wa hukumomin tsaro kan asarar soja biyar da dan sanda daya da maharan suka kashe a yankin  Karamar Hukumar Takum ta Jihar Taraba a ranar Talata.

Dan majalisar ya kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta umarci hukumomin da abin ya shafa da su kai kayan agaji ga wadanda hare-haren suka ya rutsa da su.

Shi ma d yake tsokaci, Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya yi kira ga ’yan Najeriya da su tallafa wa jami’an tsaro ta hanyar ba su kwarin guiwa da bayanan da ake bukata domin su samu damar magance matsalar rashin tsaro a Najeriya.

Shi ma da yake magana a lokacin zaman majalisar na ranar Laraba, dan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Wukari/Ibi a Jihar Taraba, Danjuma Shiddi, ya ce ’yan bindiga sun ragargaza kauyen, Tarti tare da raba daruruwan mutanen yankin da muhallansu.

Ya ce al’ummomi da dama a Takum sun fuskanci munanan hare-hare daga ’yan bindiga, na baya-bayan nan shi ne wanda aka kai ranar Talata a kauyen Tati, aka kashe sojoji shida da dan sanda daya.

Ya nuna damuwarsa kan yadda dandazon ’yan bindiga ke  da yawaita  kai hare-hare tare da lalata sassan Najeriya, don haka akwai bukatar a kara karfafa wa jami’an tsaro gwiwa.

A cikin kudurorin da majalisar ta zartar, ta bukaci Babban Hafsah Sojin Kasa, Laftanar-Janar Faruk Yahaya, da Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, Usman Baba, da su tura karin jami’an tsaro domin tabbatar da tsaron Karamar Hukumar Takum da sauran al’ummomin da ke makwabtaka da Jihar Taraba.

Har ila yau, Majalisar ta kuma bukaci jami’an tsaro da su tabbatar sun kamo masu daukar nauyin ’yan bindiga, tare da umartar Hukumar Ba da Agaji ta Kasa da ta kai wa al’ummomin da abin ya shafa tallafi.

Idan ba a manta ba Aminiya ta kawo rahoton yadda ’yan ta’adda suka kashe sojoji shida da dan sanda daya a wani rikicin kabilanci tsakanin Fulani da Kutep a kauyen Tarti da ke Karamar Hukumar.

Ana Rundunar ’Yan Sandan Jihar Taraba ta zargi ’yan sa-kan bangarorin da kisan jami’an tsaro.

Kakakin rundunar, DSP Usman Abdullahi ne ya bayyana haka yana mai cewa an tura jami’an tsaro domin tabbatar da tsaro, a yayin da ake ci gaba da neman kwamandan sojojin da