✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe mutum 6 a rikicin manoma da makiyaya a Jigawa

Sai dai ’yan sanda sun ce mutum biyu ne kawai suka mutu, wasu biyar kuma suka jikkata

Wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma ya yi sanadin kisan mutum shida tare da jikkata wasu a garin Magiram na Karamar Hukumar Guri ta jihar Jigawa.

Rahotanni daga yankin sun ce rikicin wanda ya faro tun kwanakin baya ya kazance ne ranar Juma’a, inda ya kai ga mutuwar mutanen.

Rundunar ’Yan Sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin, kodayake ta ce mutum biyu ne kawai suka mutu, wasu biyar kuma suka ji raunuka.

Kakakin Rundunar, ASP Lawal Shisu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa ranar Juma’a, inda ya ce tuni aka cafke mutum biyu, yayin da ake ci gaba da farautar sauran.

Sai dai ya ce an garzaya da ragowar Babban Asibitin garin Hadejia, inda suke samun kulawa.

Kakakin ya kuma ce suna nan suna ci gaba da farautar ragowar mutanen don tabbatar da sun shiga hannu.

ASP Lawal ya ce a ranar Juma’a ce rundunar ta samu rahoton rikicin tsakanin bangarorin biyu.

“Nan da nan muka aike da jami’anmu. Suna zuwa suka iske gawar mutum biyu; ta wani mai suna Umar Abdul Rahusa mai kimanin shekara 35 da kuma wani wanda ba a kai ga tantance shi ba. Mun kuma ceto mutum biyar da suka jikkata, kuma an garzaya da su Babban Asibitin Hadejia,” inji kakakin.

A wani labarin kuma, Kakakin ya tabbatar da cewa hankula sun fara kwanciya bayan jami’ansu sun dawo da doka da oda a yankin, inda ya shawarci mazauna garin su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum ba tare da wata fargaba ba.