✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe mutum daya a rikicin Fulani makiyaya da manoma a Ogun

Wani manomi mai suna Segun Akinlade ya ransa bayan da rikici ya barke a tsakaninsa da wani Bafulatani makiyayi a yankin Imala a jihar Ogun.…

Wani manomi mai suna Segun Akinlade ya ransa bayan da rikici ya barke a tsakaninsa da wani Bafulatani makiyayi a yankin Imala a jihar Ogun.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Ogun DSP Abimbola Oyeyemi, ya shaidawa Aminiya cewa manomin ya je gonarsa da ya share domin fara aiki sai ya hangi makiyayin a cikinta yana kiwon shanunsa, nan sai ya dauki gwafar harbin tsunsu ya sanya dutsen ya harbi makiyayin a kai lamarin da ya sanya makiyayin ya fusata ya farwa manomin da sara wanda shima a lokacin yana rike da adda a haka rikici ya barke a tsakanin su har manomin ya rasa ransa.

Ya ce, makiyayin da ake zargi mai suna Muhammad Garba, yana hannun rundunar ‘yan sandan wadanda ke ci gaba da binciken lamarin.