✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe mutum daya, an sace mutum 7 a Kaduna

Sun kawo mana harin ne haye a kan babura da tsakar rana.

’Yan daban daji sun kashe mutum daya yayin wani hari da suka kai Karamar Hukumar Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna.

Bayanai sun ce maharan sun kuma yi awon gaba da wasu mutum bakwai ciki har da mata uku.

Lamarin ya faru ne ranar Asabar a kauyen Unguwar Gajere da ke Gundumar Kutemashi na Karamar Hukumar.

Aminiya ta samu cewa, ’yan daban dajin sun kuma sace shanu bakwai kamar yadda wani mazaunin kauyen, Mohammed Birni ya tabbatar yayin ganawa da wakilinmu.

A cewarsa, “Mata uku da maza hudu da kuma shanu da dama ’yan daban dajin suka sace baya ga kisan wani mutum daya yayin harin da suka kawo da misalin karfe 1.00 na rana haye a kan Babura.

Kazalika, Kansilan Unguwar, Adamu Kutemashi, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Sai dai har yanzu Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, ASP Jalige Mohammed bai ce uffan ba, lamarin da ya ce sai ya samu cikakken bayani a kan lamarin.