✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe mutum uku a rikicin Kabilanci

Sabon rikicin da ya barke tsakanin kabilar Tibi da Jukun a garin Dananacha da ke Karamar Hukumar Gassol, Jihar Taraba, ya yi sanadiyar mutuwar mutum…

Sabon rikicin da ya barke tsakanin kabilar Tibi da Jukun a garin Dananacha da ke Karamar Hukumar Gassol, Jihar Taraba, ya yi sanadiyar mutuwar mutum uku da kone gidaje da dama.

Aminiya ta binciko cewar rikicin ya ruru ne sakamakon wata arangamar da ta kaure tsakanin matasan kabilun biyu.

An ce dattawan kabilun biyu sun shiga tsakaninsu, aka sasanta, amma kuma rikicin ya sake barkewa a ranar Alhamis.

Garin na Dananacha ya sha fama da rikice-rikice tsakanin kabilun biyu, wanda ya yi sanadiyyar mutuwa daruruwan mutane, tare da asarar dukiyoyin miliyoyin Naira.

A halin da ake ciki, garin ya rabu kashi uku; inda bangare daya ke karkashin kulawar kabilar Jukun, sauran bangarorin biyu kuma na karkashin kulawar kabilun Tibi da Hausa/Fulani.

Wani shaida, Musa Rabiu, ya fada wa wakilinmu cewar gardamar sauye-sauyen sunan garin daga Dananacha zuwa Kwararrafa ne ta haddasa rikicin.

Rabilu ya ce, a halin da ake ciki, mata da yara sai hijira suke yi daga garin domin su kauce wa barkewar sabon rikici.

Ya kuma koka kwarai da cewa an kwashe shekaru da dama ana rikicin tsakanin kabilun biyu amma gwamnati ta kasa daukar mataki ko hukunta masu haddasa fitina a garin.

Ya kuma ce kowanne daga cikin kabilun yana da sojojin sa kai da suke kai wa kauyukan junansu hari.

Da wakilinmu ya tuntubi kakakin Rundunar ‘Yan Sanda na Jihar Taraba, David Misal, ya tabbatar da an yi harbe-harbe tsakanin kabilar Tibi da Jukun amma ya ce ba a samu mutuwa ba.

Ya ce ‘yan sanda sun shiga tsakani, kuma an samu zaman lafiya.