✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe shugaban kungiyar Miyyeti Allah a Kaduna

Maharan sun nemi ya ba su Naira miliyan 20 don fansar rayuwarsa.

Wasu ’yan bindiga sun kashe shugaban kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah a Karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna, Abubakar Abdullahi.

’Yan bindigar Miyetti Allah sun kai harin ne da talatainin dare kafin wayewar garin Juma’a, kamar yadda kakakin kungiyar a Jihar Kaduna, Ibrahim Bayero-Zango, ya tabbatar.

Bayero-Zango ya ce maharan sun kai farmaki a gidan shugaban, wanda aka fi sani da Dambardi, a garin Lere ne da misalin karfe 1:00 na dare.

Ya kara da cewa ’yan bindigar sun nemi marigayin ya ba su Naira miliyan 20, kafin su dauke shi zuwa inda suka kashe shi a kan babbar hanyar Saminaka zuwa Zango.

Ya ce, “Da sanyin safiyar yau, daya daga cikin mambobinmu ya kira don sanar da shugabancin Miyetti Allah reshen Jihar Kaduna cewa da misalin karfe 1:00 na daren (Juma’a), wasu ’yan bindiga sun kai hari gidan shugaban kungiyar da ke Lere, sun kashe shi.

“A lokacin da suka isa gidan da misalin karfe 1:00 na dare, sun nemi ya ba su Naira miliyan 20 domin ya tsira da ransa amma ya ce musu ba shi da wannan kudi.

“Duk da ya samu damar ba su N250,000, amma sun kai shi bayan garin a kan babbar hanyar Saminaka zuwa Zango inda suka harbe shi har lahira,” a cewarsa.

Kakakin na Miyetti Allah ya yi Allah wadai da harin, sannan ya yi kira ga Gwamnatin Jihar da hukumomin tsaro da su yi bincike kan harin don gano wadanda suka aikata kisan.

“Mun yi tir da wannan mummunan aiki kuma muna rokon gwamnatin jiha da ’yan sanda da su gudanar da bincike kan harin, tare da gano maharan.

“Lere na daya daga cikin yankunan da ake zaman lafiya a jihar nan, babu batun rikicin makiyaya da manoma ko satar shanu a yankin, amma abun mamaki a ce an kashe shugaban Miyetti Allah, babban mai goyon bayan samun zaman lafiya a Lere.

“Muna bakin cikin faruwar wannan lamari, muna cike da bakin ciki,” inji shi.