✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe Soja 5, kwamandansu ya bace a rikicin Taraba

Sojojin da kwamandan nasu sun fito ne daga Bataliya ta 93 da ke Takum.

An kashe soja shida da dan sanda daya a yayin da kwamandan sojojin ya yi batar dabo a wani rikicin kabilanci a Jihar Taraba.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Taraba ta tabbatar cewa sojojin da aka kashe da kwamandan nasu da ya bace sun fito ne daga bataliya ta 93 da ke Karamar Hukumar Takum ta jihar.

Kakakin rundunar, DSP Usman Abdullahi, ya ce jami’an tsaron sun gamu da mummunar kaddarar ce a rikicin kabilanci tsakanin Kutep da Fulani a yankin Tarti da ke Karamar Hukumar Takun ta jihar.

Da yake bayani kan mutuwar sojojin da bacewar kwamnandan mai suna Laftanar Kanar Eminike, DSP Abdullahi, ya ce Laftanar Kanar Eminike ne ke jagorantar sojojin jami’an tsaron a aikin samar da tsaro a yankin da rikicin ya barke.

DSP Usman ya zargi ’yan sa-kan kabilun Kutep da Fulani da kashe jami’an tsaron, amma an tura karin jami’an tsaro yankin sun kuma tsananta neman kwamandan da ya bace.

Ya bayyana cewa a ’yan makonnin da suka gabata, ’yan sa-kan kabilun sun yi ta rikici a tsakaninsu, wanda ya kazance a ranar Talata, wanda ya sa aka tura karin jami’an tsaro domin tabbatar da doka da oda.

A cewarsa, kawo yanzu, ba za a iya tantance adadin mutanen da aka kashe a rikicin ba.

Wannan na zuwa ne wata guda bayan an kashe wadansu ’yan sanda uku a lokacin wani rikicin kabilancin Kutep dan Jukun kan bikin al’adar Kutep na shekara-shekara.