✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe sojoji 11 a bakin aikinsu a Binuwai

Rundunar Soji na neman wadanda suka kashe hafsanta daya da kananan sojoji 10 ido rufe

Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta ce wasu bata-gari da ba a gano ko su wane ne ba sun kashe dakarunta 11 a Jihar Binuwai.

Kakarin Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, Manjo Janar Mohammed Yerima ya ce hafsan soji daya da kananan sojoji 10 din sun rasu ne a yayin da suke aikin tabbatar da zaman lafiya a Binuwai.

Ya ce da farko Rundunar ta yi zargin sojojin 11 da suka hada da masu aiki a rundunar Operation Whirl Stroke sun bace ne, amma daga baya ta gano su an kashe su a Karamar Hukumar Konshisha ta Jihar, inda aka kwashe gawarwakin sojojin, aka kuma fara bin sawun miyagun domin a kamo su, su dandana kudarsu.

“Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya na rokon jama’a cewa duk mai wani bayani da zai iya kai ga kamo miyagun da suka yi wannan danyen aiki da ya taimaka mata,” inji sanarwar da Yerima ya fitar.

Ya ba da tabbacin ceaw abin da ya faru da sojojin ko harin da ake kai musu ba zai hana Rundunar ci gaba da aikinta na tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Jihar ta Binuwai ba.

“Sanin kowa ne cewa an samu zaman lafiya daidai gwargwado a Jihar Binuwai mai fama da rikice-rikice, sakamakon nasarorin da hukumomin tsaro suka samu a aikinsu, ba dare, ba rana, na tabbatar da tsaro da aminci daga ayyukan miyagu,” inji shi.