✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe tsohon hakimi a kudancin Kaduna

A daren Litinin ne wasu mahara da ba a san ko su waye ba suka kai hari gidan tsohon hakimin Jagindi Tasha da ke garin…

A daren Litinin ne wasu mahara da ba a san ko su waye ba suka kai hari gidan tsohon hakimin Jagindi Tasha da ke garin Dangwa a masarautar Godogodo a karamar hukumar Jama’a ta jihar Kaduna, inda suka bindige shi har lahira shi da dan uwansa.

Tsohon hakimin, Danlami Barde, ya mutu nan take, yayin da dan uwan nasa Musa (Moses) Barde ya cika bayan an kai  shi asibitin Kowa Medical Center da ke Godogodo, kamar yadda wani mazaunin garin na Dangwa, Marshall Ibrahim, ya shaidawa Aminiya ta wayar tarho.

Marshall ya ce suna zaune da misalin karfe 8:45 na dare sai suka fara jin harbin bindiga.

“Mun arce don neman mafita amma daga baya sai muka fahimci gidan tsohon hakimin kawai suka kai wa hari inda suka yi nasarar kashe shi tare da dan uwansa, sannan suka raunata matarsa mai suna Hajiya Ishaku.”

A labarin da Aminiya ta tattara, an ce an kai wa tsohon hakimin hari ne a daidai lokacin da suke zaman yin sulhu don sasanta wani rikici, sai maharan suka diro cikin gidan suka bude musu wuta.

Yayin da yake yi wa Aminiya karin haske bayan ya tabbatar da faruwar lamarin, Shugaban Karamar Hukumar Jama’a, Peter Danjuma Averik, ya ce tuni jami’an tsaro suka shiga garin don tabbatar da zaman lafiya tare da binciken lamarin.

Sannan shugaban ya yi kira ga jama’ar yankin da su kai zuciya nesa yayin da da ake gudanar da bincike a kan musabbabin harin da kuma gano ko su waye su ka kai shi.

A halin yanzu an kai gawar hakimin da ta dan uwansa dakin ajiye gawarwaki na Asibitin Tunawa da Patrick Ibrahim Yakowa da ke garin Kafanchan, yayin da ita kuma uwargidan hakimin aka wuce da ita zuwa wani asibiti da ba a bayyana ba don ci gaba da kula da ita.