✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe wadanda suka fasa gidan yarin Owerri

’Yan sandan sun hallaka bata-garin ne bayan musayar wuta.

’Yan sanda sun bindige mutum biyu daga cikin wadanda suka kitsa harin da aka kai aka fasa Gidan Yarin Owerri da ke Jihar Imo.

A lokacin tarzomar EndSARS ne bata-gari a Jihar Imo suka balla gidan yarin na Owerri, wanda kusan daukacin fursunoni suka tsere illa ’yan kalilan.

Amma a wani samame a daren Talata, ’yan sanda sun harbe mutum biyu da ake zargi da balla gidan yarin.

Bayan musayar wuta ta kusan awa biyu a yankin Ocha da ke Karamar Hukumar Bema, Rundunar ’Yan Sandan Jihar Imo ta gano bindiga kirar Ak 47 guda daya da harsasai masu tarin yawa da adduna da layu a tare bata-tarin da ta hallaka.

Kakakin Rundunar, SP Bala Elkana, ya ce za a ci gaba da kai irin samamen domin tabbatar da hukunta wadanda suka fasa gidan yarin.