✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kashe ’yan bindiga 3 an ceto mutum 7

’Yan sanda sun kashe ’yan bindiga uku tare da ceto mutum bakwai da aka sace.

’Yan sanda sun kashe ’yan bindiga uku tare da ceto mutum bakwai da aka yi garkuwa da su.

Hadin gwiwar ’yan da ’yan bangar sun samu nasara ce a ci gaba da sharar dajin da suka kubutar da wasu matafiya 13 da aka yi garkuwa da su a karshen mako.

Jami’an tsaron sun matsa kaimi da aikin sintirin ne a yankin Ahor da ke kan hanyar Benin zuwa Legas a Jihar Edo, inda aka yi garkuwa da matafiya 13 a ranar Alhamis.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Edo ta ce jami’anta da ’yan bindigar sun yi arba da ’yan bindigar ne a Ahor, yayin neman wadanda yi garkuwa da su.

Kakakinta, SP Kingtongs Bello, ya ce da ganin jami’an tsaron sai masu garkuwar suka bude musu wuta, nan take suka mayar da martani suka bindige uku daga cikinsu.

Ya ce mutum bakwai da aka ceto su ne Daniel Musa, Anslem Obaladike, John Rufus, Best Osarenrere, Okideli Uwachukwu, Unoma John da kuma Festus Francis.