✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe ’yan daba biyu a artabu da ’yan sanda

Bata-gari biyar sun shiga hannu, bayan da ’yan sanda suka aika biyu daga cikinsu lahira.

Akalla mutum biyu ne suka mutu yayin da wani rikicin ’yan daba ya barke a yankin Arulogun da ke garin Ed na Jihar Osun.

Kakakin ’yan sandan jihar, Yemisi Opalola, ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Juma’a, inda ya ce tuni aka cafke mutum biyar daga cikin bata-garin.

Sai dai ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a samu cikakken rahoto game da hakikanin abin da ya faru ba.

Sai dai wani rahoto ya ce wasu bata-gari 30 sun yi wa gidan Wakili Olayiwola kawanya, suna fara harbe-harbe suka kuma kona motarsa.

Sai dai jami’an ’yan sanda sun isa wurin a kan lokaci, inda suka rika  dauki ba dadi da ’yan daban  har sai da suka ci karfinsu.

Kakakin ’yan sandan, ta bayyana cewar jami’ansu sun yi nasarar kashe biyu daga ’yan daban, tare da cafke biyar daga cikinsu.

Ta kara da cewa an kai gawar mutum biyu da suka kashe a dakin ajiye gawa, don ci gaba da bincike.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Wale Olokode, ya ba da umarnin tsaurara bincike tare da kamo ragowar bata-garin da suka tsere, don gurfanar da su gaban kotu.