✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe ’yan sanda 3 suna tsaka da binciken ababen hawa

Maharan sun kashe wata mata sunnan yi awon gaba da wata mota da kudade.

Rundunar ’yan sandan Jihar Enugu ta tabbatar da kisan jami’anta uku da wasu mahara suka yi a ranar Alhamis, a yayin da suke tsaka da aikin binciken ababen hawa.

An shiga rudani da fargaba a cikin garin Enugu bayan da maharan suka kashe jami’an ’yan sandan uku.

Lamarin ya faru da misalin karfe 1:20 na ranar a yankin Ulumalinda da ke Karamar Hukumar Enugu ta Kudu a jihar.

Maharan sun dauki tsawon minti 30 suna sharafinsu ba tare da an samu dauki daga jami’an tsaro ba, kafin daga bisani su yi awon gaba da wata mata da ba a bayyana sunanta ba.

Kazalika, kafin su fice daga yankin sun shiga shagon wata mata da ke hada-hadar kudi ta POS inda kwashi kudi sannan suka harbe ta da bindiga.

Kakakin ’Yan Sandan Jihar Enugu, Daniel Ndukwe, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ce suna gudanar da bincike a kai.