✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kashe ’yar abokin Putin a Moscow

Ana dai zargin mahaifin nata aka yi yunkurin hallakawa a harin

Wani bam da aka dana a jikin mota a birnin Moscow ya hallaka diyar wani da ake rade-radin aboki ne na kusa ga Shugaban Kasar Rasha, Vladimir Putin.

Rahotanni sun ce an kashe Darya Dugina ne a wani harin da aka yi kokarin kai wa kan mahaifin nata.

Mai kimanin shekara 29, Darya ta mutu ne bayan bam din ya tarwatsa motar da take ciki kirar Toyota Land Cruiser, lokacin da take tafiya da daren Asabar, kamar yadda wata sanarwa ta tabbatar a ranar Lahadi.

Darya dai diya ce ga Alexander Dugin, wani wanda ya jima yana neman ganin an hade kan yankunan da ke amfani da harshe Rashanci a matsayin sabuwar daula guda daya.

An kuma yi ittifakin yana daya daga cikin masu matukar tasiri wajen saita tunanin Shugaba Putin a kan manufofin Rasha a kasashen waje, da ma musamman yakinta da Ukraine.

Kamfanin dillancin labaran Rasha (TASS), ya rawaito cewa motar mallakin mahaifin nata ce, kuma shi aka yi yunkurin hallakawa a harin.

Sai dai har yanzu babu wanda ya dauki alhakin kai harin.

Jaridar Rossiiskaya Gazeta, mallakin gwamnatin Rasha ta ce diyar tare da mahaifin nata sun halarci wani bikin al’ada ne a wajen birnin Moscow, kafin daga bisani su yanke shawarar yin musanyen mota gabanin faruwar lamarin.

Tuni dai masu bincike suka ce sun dukufa wajen ganin sun gano musabbabin harin da kuma masu hannun a cikinsa.