✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe ’yar aiki da duka a Filato

Galibin yaran da ake dauka ana tura su aikatau a gidaje sukan fuskanci muzgunawa, walau daga wajen wadanda suke yi wa aikin, ko daga wajen…

Wata ’yar aiki ta riga mu gidan gaskiya sakamakon dukan da iyayen-gijinta suka lakada mata.

An tabbatar da mutuwar yarinyar mai suna Margaret ne a Asibitin Koyarwa ta Jami’ar Jos (JUTH).

Rahotanni sun ce, Margaret ta mutu ne sakamakon raunukan da ta ji a dalilin dukan da ci a hannun ma’auratan da take yi wa a iki a yankin Vom, cikin Karamar Hukumar Jos ta Kudu.

An ce rashin kula da raunukan da marigayiyar ta ji ya sa kwayoyin cuta suka samu shiga cikinta tare da yin ajalinta.

Ana zargin cewa, ba yau ne farau ba, wadanda ake zargi da kashe yarinyar sun saba gana mata azaba.

Hukumar Kula da Hakkin Dan Adam ta Kasa (NHRC) a Jihar Filato, ta tabbatar da aukuwar lamarin.

Hukumar ta ce ta gano an yiwo safarar marigayiyar daga Jihar Kebbi ne sannan aka damka ta ga wadanda take yi wa aiki.

Mai magana da yawun ’yan sandan jihar, DSP Alfred Alabo, ya ce an damke matar da ake zargi da hannu cikin mutuwar yarinyar an kuma fara bincike kafin daga bisani a gurfanar da ita a kotu.